Kansila a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara Sirajo Madugu ya bayyana cewa sansanonin ‘yan gudun hijiran dake jihar na kara cika da masu neman mafaka.
Ya ce dalilin haka kuna na da nasaba ne da karuwar aiyukkan maharan dake addabar mutanen kauyukan jihar.
Madugu ya ce akalla kauyuka 50 ne mahara suka wargaza a fadin jiha sannan wasu da yawa sun gudun daga garuruwan su ne saboda tsoron kada a far musu.
” Har yanzu bamu da hakikanin yawan mutanen da suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijiran domin har yanzu ana daukar sunayen su ne.
A karshe shugaban karamar hukumar Maradu Yahaya Shehu ya yi kira ga ‘yan gudun hijiran da su kai karan duk wanda ba su amince da shi ba domin hakan zai taimaka wajen dakile duk wani shira na masu son tada zaune tsaye a jihar.
Ya kara da cewa gwamnati zata ci gaba da samar wa mazauna sansanonin tallafi.