Yadda Lawal Daura ya rika karbar buhunan daloli na cin hanci, yana yi wa Buhari Zagon Kasa

0

Wani Mataimakin tsohon shugaban Hukumar SSS, Lawal Daura, Abdulwahab Abdulrahman ya tona asirin korarren shugaban hukumar cewa daya daga cikin dalilan da ya sa ya ajiye aiki shine yadda Daura yake karbar cin hanci da rashawa kamar babu gobe a hukumar.

Saboda haka ni Abdulrahman na sama wa kai na lafiya, na tattara nawa-ina-wa na ajiye aikin saboda kada watara ‘ya’ya na su ganni a Talabijin an tasa keya na zuwa kurkuku.

” Jim kadan bayan mun fara aiki a hukumar SSS, Daura yace ya ai sai mu rubuta wa Buhari a bamu naira biliyan 1 domin fara aiki. Tun daga nan nace ina Buhari ya ga naira biliyan 1.

” Dama can fa Buhari ba wai ya san Lawal daura bane, a 2015 ne lokacin Kamfen ya san shi. Sannan ko bayan da aka nemi Buhari ya nada shi Buhari bai amince ba, amma kuma da yake Mamman Daura ne ya kawo sa shine ya sa aka yi masa shugaban SSS din.

” Mu kan kai har karfe 12 da dare muna aiki, amma kun san aikin da muke yi kuwa, aikin karbar cin hanci a buhuna kawai muke yi daga wadanda ba su shiri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

” Akwai lokacin da Daura ya daina aikawa da dala wajen masu canji. Ya kare ne sai dai a kira sakataren kungiyar masu canza dala ya zo da na’urar kirga kudi ayi ta kirga su a ofishin sa.

” Bayan haka nayi ta rokon sa ya hakura ya taimaka wa Buhari, ya daina abin da ya keyi sai yayi fushi ya daina biya na fansho. Daga baya da nayi barazanar maka shi a kotu sai ya tsorata ya fara biya na.

” Idan mataimakin shugaban kasa ya bukaci ya bayyana a ofishin sa ba ya zuwa a kan lokaci. Kuma ida ma ya zo bazai roki gafara ba. Akwai lokacin da suka yi cacan baki da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, da sai da shi kan sa mataimakin shugaban Kasa ya raba su.

” Sannan akwai lokacin da ya kira Sambo Dasuki, ya ci masa mutunci, Dasuki ya gargade sa cewa ya bi duniya a hankali, domin rayuwa juyi-juyi ne, wata rana zai iya samun kan sa a inda ya ke.” Inji Abdulrahman.

Share.

game da Author