Kungiyar Tarayyar Turai(EU), ta nuna matsananciyar damuwa dangane da yadda jami’an SSS suka mamaye Majalisar Tarayya, har kungiyar ta yi gargadin cewa jami’an tsaro su guji nuna bangaranci wajen amfani da kayan gwamnati.
“Kungiyar ta ce akwai damuwa sosai idan aka buga misali da yadda ake amfani da jami’an tsaro wajen yi wa dimokradiyya kutse – kamar yadda jami’an SSS suka kewaye Majalisar Tarayya a ranar 7 Ga Agusta,”.
Haka kungiyar ta EU ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta aiko wa PREMIUM TIMES a yau Alhamis da safe.
“EU ta maida hankalin ta sosai wajen tallafa wa da goyon bayan tsarin dimokradiyya a Najeriya, kuma ta jinjina wa Gwamnatin Najeriya dahngane da yadda ta gaggauta daukar matakinn kare dimokradiyya.”
Haka ya ke a rubuce, cikin bayanin da kakakin yada labaran kungiyar a nan Najeriya, a Abuja.
Haka nan shi ma ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya, ya yi Allah-wadai da mamayar da SSS suka kai wa Majalisar Tarayya, a cikin wani jawabi da ofishin ya fitar a ranar Talatar da abin ya faru.
Birtaniya ta ce ba za ta taba amincewa da duk wani yunkuri na keta haddin dimokradiyya ba.