Wasu likitoci da suka gudanar da bincike kan cutar Kanjamau a kasar Amurka sun bayyana cewa ba a kamuwa da cutar ta hanyar sumbatar mace ko namijin da ke dauke da cutar.
Likitocin sun kuma kara da cewa idan har mutum na kiyaye dokokin ta kamar shan maganin kamar yadda a ka ce zai yi rayu kamar yadda sauran mutanen da basu da cutar ke rayuwa.
” Hakan na nufin cewa baza a iya kamuwa da cutar daga jikin wanda ke kiyaye dokar shan magani da kula da lafiyar sa ba sannan macen da ta kiyaye wannan doka na iya shayar da danta nono ba tare ya kamu da cutar ba.”
Sun yi kira ga duk wanda ke dauke da Kanjamau da ya maida hankali wajen kiyaye shan maganin, cewa idan haryayi haka zai rayu kamar sauran mutanen da ba su dauke da shi cutar suke rayuwa.