Sojojin Najeriya sun bayyana kashe mahara 20 a jihar Zamfara, wadanda ta ce an kashe su a ranar Asabar, kuma ta ceto wadanda suka yi garkuwa da su.
Sojojin na ‘Operation Sharan Daji, sun bayyana haka ne ta hannun kakakin yada labaran su, Muhammed Dole, a cikin wani jawabi da yafitar yau a Kaduna.
Ya ce sun share maharan 20 ne a wasu hare-hare mabambanta a sansanonin su da ke dazukan Maradun, Tsafe da Zurmi a jihar Zamfara.”
Ya ce an kashe wasu a kauyen Daban-Doka, kusa da Dansadau, inda a can ne aka kashe mahara 20 din.
“Wasu daga cikin su sun tsere da raunuka sakamakon harbin da aka yi musu, yayin da aka kona baburan su da dama.
An kuma kashe wani gogarman su mai suna Bello Danboko da Sani Maza a Yanwari kusa da Yankuzo da kauyen Mai Tunkiya da ke kusa da Dansadau.”
Ya ce an kuma yi batakashi da maharan a kauyukan Mashema, Kwadi, Kalage, Gambiru da hanyar ficewa zuwa Kagara.
Kakakin ya kara da cewa an kuma banka wa matsugunan su da dama wuta sun kone kurmus.
Ya ci gaba da cewa wannan nasara da aka samu ta sa wadanda ke sansanin gudun hijira zuwa kauyukan su na cikin Karamar Hukumar Zurmi.
“An kuma tsananta sintiri a kauyukan Kyaranke, Giwabawa da ke cikin Masarautar Kanoma da ke karamar hukumar Maru, saboda an ji labarin maharan har sun fara aza harajin naira milyan daya a kowane kauye.
“Wani bin-sayu da aka yi kuma ya haifar da ceto wasu da aka yi sannan kuma an samu kudi har naira dubu 500 daga hannun su.
Discussion about this post