Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa shugabannni nagari kuma wadanda suka san kan mulki Najeriya ke bukata, ko da ba su da wani karfin kuzari.
Jega ya yi wannan kalami ne jiya Litinin a wurin taron Shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyi ta Kasa.
Jega ya ce idan aka ce shugaba mai karfi ne, to idan fa bai cancanci iya rike mulki ba, zai yi amfani ne kawai da karfin sa ya lalata tsarin mulki da gwamnati gaba daya.
“Abin da muka fi bukata shi ne shugabanni masu sanin ya kamata tare da cancantar rike ikon da ya rataya a kan su, wadanda za su iya bugun kirjin daukar wata matsaya ko wani batu tare da tabbatar da cewa su ga an yi duk abin da suka bada umarni a yi. To don haka mu yi taka-tsantsan wajen yin gurgun tunanin ma’anar da ake nufi da shugaba mai karfi.
“Kamar shugaba maras karfi shi ma zai lalata turbar mulki da shugabanci ne kawai. Haka shugaba mai karfi idan ba shi da sanin-makamar-mulki ko shugabanci, shirme da tabargaza kawai zai rika yi.
“Don haka cancanta ko sanin-madafar-shugabanci na da muhimmancin gaske wajen gina ingantacciyar dimokradiyya, kwakkwarar gwamnati da kuma kara wa bangon dimokradiyya karfin da za a ji dadin jingini a jikin sa.” Inji Jega.
Daga nan sai Jega, wanda shi ne ya gudanar da zabukan 2011 da 2015, ya ce ya zama dole sai ‘yan siyasa su daina daukar zabe a matsayin wani abu na ko-a-ci-ko-a-mutu.