SERAP ta maka Hukumar NYSC kotu saboda kin yin bayani kan Minista Adeosun

0

Kungiyar Rajin Tabbatar da Ka’ida da Dokoki, SERAP, ta maka Hukumar Aikin Bautar Kasa, NYSC kotu, saboda kin yi wa jama’a bayanin sahihanci ko rashin sahihancin satifiket din jabu da aka zargi Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta mallaka.

Premium Times ce ta rika fallasa labarin yadda Adeosun ta ki yin aikin bautar kasa, daga baya kuma ta bi ta karkashin kasa ta karbi katin shaidar yafe mata aikin bautar kasa ba bisa ka’ida ba.

A yanzu SERAP ta garzaya kotu, bayan da ta ba NYSC wa’adin mako daya ta yi bayani, ganin an wuce wa’adin babu wani ba’asi daga hukumar, sai SERAP ta garzaya kotu.

A cikin kwafen karar da aka shigar, mai lamba FHC/L/CS/1369/18 da aka shigar yau Talata a Babbar Kotun Ikeja da ke Lagos, SERAP ta nemi kotu ta tilasta Darakta Janar na Hukumar NYSC, Janar Kazaure da ya bayar da dukkan bayanan da ake nema dangane da Kemi Adeosun, Ministar Kudaden Najeriya.

SERAP ta kuma nemi hukumar NYSC ta buga dukkan bayanan na Kemi Adeosun a jaridu har a shafin intanet na NYSC domin kowa ya gani.

Lauyan kungiyar SERAP mai suna Bamisope Adeyanju ne ya shigar da karar a madadin SERAP, inda ya ce su na zargin daga daga cikin jami’an wannan gwamnati mai rike da babban mukami, ta aikata ba daidai ba.

SERAP ta kafa hujja da dokokin Najeriya masu lambobi 104(1) na cikin dokar 2011 da na cikin sashe na 14(b) 14(3) da kuma 19(2) da suka nuna cewa tunda NYSC hukuma ce ta gwamnati, ba ta da hujjar boye harkallar da ake zargin Adeosun ta aikata.

Ba a dai sa ranar da za a fara sauraren karar ba.

Share.

game da Author