Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare wakilin PREMIUM TIMES, Samuel Ogundipe

0

A Yau Talata ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare daya daka cikin wakilin jaridar PREMIUM TIMES mai suna Samuel Ogundipe a hedikwatar ta na SARS dake Abuja.

Babban dalilin da yasa ake tsare Samuel kuwa shine wai suna so ya bayyana musu asalin inda ya sami bayanai na wani labari da jaridar ta wallafa a makon da ya gabata, duk da cewa bayanan haka ne, yadda ya sami bayanan suke so su sani. Sai dai kuma doka ta hana haka.

Duk da cewa ba jaridar bane kawai ta rubuta wannan labari, Rundunar ‘yan sanda ta karkata zuwa ga jaridar domin wani shiri na yi mata bita da kulli.

A hedikwatar ‘yan sandan, tare da babban editan jaridar Mojeed Musikilu, ya yi kokarin bayyana wa jami’an ‘yan sandan cewa doka ta ba dan jarida kariya na kada ya fadi inda ya samu bayanan sa musamman idan abin babu kuskure a ciki.

Share.

game da Author