A sanarwa na musamman da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Magaji Majiya ya fitar ranar Juma’a a garin Kano rundunar ta gargadi mazauna garin musamman matasa cewa daga yanzu an hana bukin hawan dokin kara da ake yi a wasu unguwannin jihar.
Magaji ya kara da cewa duk wanda aka kama ya na yin wannan hawa zai kuka da kan sa.
Sanarwar ya kara da cewa haramta wannan hawa ya shafi dukkan unguwannin cikin birnin jihar da kewaye.
” Wannan hani ya zama wajibi duba da yadda samari suke gangamin shirya irin wannan hawan kuma daga karshe yake haifar da fadace-fadacen Daba da kuma tunzuri bayan muzgunawa al’umma babu gaira babu dalili.
” Haka zalika, an samu Shugabannin Al’umma daban-daban da suka yi korafin wannan Hawa da yake Uzzurawa Al’umarsu.
” A sakamakon haka, Rundunar ta hana duk wani Hawan Dokin Kara da aka shirya a Jihar Kano har sai Baba ta gani.
” Kuma an baiwa Baturan Yan Sandan Jihar Kano umarnin karsu kara karba ko amincewa wadanda suka rubuto takardar neman izinin gudanar da Hawan Dokin Kara.
” Da fatan Iyaye zasu gargadi Yayansu, sannan Samari su kaucewa dukkanin abinda ya saba tsarin doka da kuma abinda zai haifar da tashin hankali, Asarar Rayuka, da Dukiya ko kuma tashin tashi na.
” Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira, haka kuma idan an ki ji, to ba’a ki gani ba.
Discussion about this post