A ci gaba da tsare wakilin jaridar PREMIUM TIMES Samuel Ogundipe da rundunar ‘Yan sandan Najeriya ke yi, ranar Laraba da rana sun dauke shi zuwa wani kotun majistare dake unguwar Kubwa dake Abuja inda suka gurfanar dashi a gaban alkalin kotun.
Kafin su garzaya da Samuel wannan kotu, sai da suka tabbata babu yadda zai gana da Lauyar sa ko wani wakilin ma’aikatar sa wato PREMIUM TIMES kafin su tafi kotun.
Duk da cewa sun shaida wa lauyoyin PREMIUM TIMES din cewa ba a wannan lokaci za su shiga kotu da Samuel. Lauyoyin na juya baya sai suka sulale da shi zuwa kotu a Kubwa.
A kotun, Samuel ya roki alkalin kotun ya ba shi daman yin magana da Lauyan sa ko babban editan PREMIUM TIMES.
A nan ne alkalin kotun ya amince da a ba Samuel waya ya kira editan sa.
” Ga sunan sun tafi da ni a asirce zuwa kotu a Kubwa, sannan sun ce wai suna tuhuma na ne da laifin mallakar wasu takardu da bai kamata ace wai na mallake su ba. Suna tuhuma na da laifin sata. Amma kuma basu gaya wa alkalin ni dan jarida bane.” Inji Samuel.
Kafin Samuel ya kammala magana, sai suka kwace wayar, sannnan Alkali ya yanke hukuncin da aci gaba da ajiye shi har sai 20 ga watan Agusta.
Jaridar PREMIUM TIMES ta yi kira da kakkausar murya ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta gaggauta sakin daya daga cikin wakilin ta dake tsare a hedikwatar hukumar.
A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare daya daka cikin wakilin jaridar PREMIUM TIMES mai suna Samuel Ogundipe a hedikwatar ta na SARS dake Abuja.
Babban dalilin da yasa ake tsare Samuel kuwa shine wai suna so ya bayyana musu asalin inda ya sami bayanai na wani labari da jaridar ta wallafa a makon da ya gabata.
Hukumar ‘Yan sanda sun nemi Samuel ya bayyana musu wanda ya bashi wadannan takardu da Sifeto Janar Idris Ibrahim ya mika wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
A wasikar, Sufeto Ibrahim ya bayyana yadda Lawal Daura ya rika cin karen sa babu babbaka a hukumar SSS da ya shugaban ta.
Duk da cewa ba jaridar bace kawai ta rubuta wannan labari, Rundunar ‘yan sanda ta karkata zuwa ga jaridar domin wani shiri na yi mata bita da kulli.
A hedikwatar ‘yan sandan, tare da babban editan jaridar Mojeed Musikilu, ya yi kokarin bayyana wa jami’an ‘yan sandan cewa doka ta ba dan jarida kariya na kada ya bayyana inda ya samu bayanan sa, Sannan ya yi musu tuni da hakan da suke bukata daga wurin Samuel zai iya tozarta Najeriya a Idanun duniya. Da bude bakin sa dan sandan dake tare da su a wannan ofishi mai mukamin DCP, cewa yayi shi fa ‘Najeriya ba ta dame shi bane. Kawai abin da yake so a gaya masa inda aka samu wannan bayanai.
PREMIUM TIMES ta yi kira ga mukaddashin shugaban kasa da ya gaggauta bada umarni a saki wannan wakili na ta wato Samuel Ogundipe.
Bayan haka, kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya sun yi tir da wannan abu kuma sun yi kira da a gaggauta sakin dan jaridar.
Jim kadan bayan sun tsare Samuel Ogundipe, sai kuma aka kulle asusun ajiyar sa na banki. Da shima haka saba dokar kasa ce.