Rikicin Zamfara ya ci rayuka 3,000, ya tada gidaje 2,000 – Gwamnati

0

Kashe-kashen farmaki da mahara ke yi a Jihar Zamfara, ya janyo asarar rayuka sama da 3,000, yayin da aka lalata gidaje sama da 2,000. Wani jami’in gwamnatin Jihar Zamfara din ne ya bayyana haka.

Sakataren Gawamnatin Jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, a Gusau, a wani taron ganawa da juna a dakin taron Gusau, wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta shirya.

Shinkafi ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da naira bilyan 17 wajen kokarin shawo kan wannan matsala ta masu kashe jama’a a jihaar, a cikin shakaru bakawai zuwa yau.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya,NAN, ya ruwaito yadda taron ya kaya, inda ya ce an kira taron ne domin gano kan bakin zaren yadda za a shawo kan wannan matsala, ganin yadda sai tsaro ke kara tabarbarewa a jihar.

Shinkafi ya ce baya ga kisan sama da mutum 3,000 da kone gidaje sama da 2,000, wannan rikici ya kawo asarar sama da motoci 500 da aka kona. An kuma yi garkuwa da mutane sama da 500 wadanda ake kamawa ana neman a biya diyya kafin a sake su.

Daga nan ya ce ana kashe kudaden daga 2011 zuwa yau, wajen sayen motocin jami’an tsaro, biyan kudaden alawus din su, samar musu matsuguni ko sansanoni, da sauran hidindimun kashe kudaden yau da kulllum.

“Na san idan ku ka ji an ce an kashe har naira biliyan 17 za ku ji abin bambarakwai. Amma idan ka fara yi wa wannan adadin kudade dalla-kuma filla-filla, zaka ga ma sun yi kadan.

“Cikin 2011, mun sayo wa jami’an tsaro motoci 457, cikin 2012 kuma mun sayo motoci 2,250, cikin 2014, mun sayo motoci 77. Sannan kuma tsakanin 2015, 2016, 2017 da 2018, a kowace shekara sai mun sayi motoci 50.

“Sannan kuma wadanda aka kai wa harin nan muka bi su mu ba su wani dan tallafi, akalla domin dai yi musu wani agaji.”

Shinkafi nya ce jihar Zamfara ta dade cikin wannan mummunan hali, don haka akwai bukatar al’umma da kuma gwamnatin tarayya su kara himma wajen nuna damuwa da kuma gano hanyar shawo kan wannan fitina, tun kafin ta kara karfin da za a kasa maganin ta.

Ya tunatar cewa wannan rikici ya fara ne daga fada tsakanin makiyaya da manoma, amma sai mahara da muggan ‘yan fashi suka yi uwa makarbiya, inda suke kai wa al’umma munanan hare-hare, da ya ce an yi sun kai 40.

Ya roki iyaye su kula da ‘ya’yan su, su kuma maza su daina auren mata da yawa idan ba su da halin daukar dawainiyar iyali masu yawa.

Ya ce saboda idan ka tara yaran da ba ka iya kula da su, sai ‘yan ta’adda su kwace maka su dora su kan mummunan hanya.

Daga nan ya kara yin kira ga matasan jihar Zamfara da su shiga ayyukan jam’ian tsaro domin bada ta su gudummawar.

Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Abubakar Mahmud, ya yi mamakin yadda gwamnatin tarayya za ta kyale jiha da nauyin kashe makudan kudade wajen kula da tsaron, jihar, wanda ya ce aiki ne da ya rataya a kan gwamnatin tarayya.

Daga nan sai ya jinjina wa gwamnatin Adulaziz Yari kan yadda ta dauki neman shawo kan kashe-kashen da muhimmanci.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin har da tsohon sanata Sa’idu Dansadau. Daga nan kuma kungiyar lauyoyin ta kai ziyara ga Sarkin Zurmi.

Share.

game da Author