R-APC ta zargi jam’iyyar APC da kokarin raba wa sanatoci naira miliyan 50 kowanen su, domin su tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, wanda ya fice daga APC.
Kakakin R-APC, Kassim Afegbua ne ya bayyana haka a cikin wata takardar da ya fitar wa manema labarai.
Sai dai kuma Afegbua bai bayar da wasu hujjojin sa na yin wannan zargi ba.
“Daga cikin shirin da su ke kullawa, har akwai kokarin a tuntubi wasu sanatocin PDP, musamman wadanda ke da igiyar EFCC a wuyan su, cewa idan suka fice daga PDP suka koma APC, to a za wanke laifukan su komai girman sa.
“Sannan kuma sun amince su bai wa wasu sanatocin naira miliyan hamsin kowanen su.”
Sai dai kuma wannan kungiya ta ce ai akwai hanyoyin da ake bi domin a tsige shugaban majalisar dattawa, wacce ita kadai ce amintacciyar hanyar da za a iya tsige shi.
R-APC ta ce an kitsa wannan tuggun yunkurin tsige Saraki da karfin tuwo ne a gidan Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole, da ke unguwar Maitama, Abuja.
Afegbua ya ci gaba da cewa sun shirya idan har yunkurin ya yi nasara, to wai Sanata Abdullahi Adamu ne zai maye gurbi Saraki.
A karshe ya ce ana kuma kokarin yadda za a samu wani alkalin da zai halasta tsige Saraki da gaggawa, da zaran an tsige shi din.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta karyata wannan zargi da cewa soki-burutsu ne kawai babu wani kamshin gaskiya ko kadan a cikin sa.
Discussion about this post