Jam’iyyar PDP ta yi kira da kakkausan harshe cewa a gaggauta bude asusun ajiyar jihohin Akwa-Ibom da Benuwai, wadanda Hukumar EFCC ta toshe.
A cikin wata takardar da Sakataren PDP na Yada Labarai, Kola Ologbondiyan ya fitar jiya Laraba a Abuja, ya ce Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya gaggauta umartar EFCC su bude asusun ajiyar kudaden jihohin guda biyu.
Ba fassara abin da EFCC ta yi da cewa wani farmaki ne aka kai wa al’ummar jihohin biyu.
Jam’iyyar PDP ce ke mulkin wadannan jihohi guda biyu. An toshe kofar asusun jihar Benuwai, bayan gwamna Samuel Ortom ya fice daga APC. Shi kuma na jihar Akwa-Ibom an toshe shi a ranar da tsohon gwamnan ya koma jam’iyyar APC, shi kuma gwamnan da mataimaki su ka ce ba za su bi Sanata Akpabio cikin APC ba.
Ologbondiyan ya ce toshe asusun gwamnatin jihar Benuwai, karya dokar kasa ce kuma tsantsar mugunta da kuntatawa ce ba tare da umarnin wata dokar Najeriya ba.
Ya shawarci fadar shugaban kasa ta daina fakewa a cikin inuwar EFCC ta na kara jefa al’ummar jihohin adawa cikin kunci, don kawai su na adawa da APC mai mulki, saboda abin duk kan zaben 2019 ta ke hari.
Discussion about this post