PDP ta fara sayar da fam ga ‘yan takarar zabe

0

Jam’iyyar adawa, PDP ta bada sanarwar fara saida fam ga dukkan masu sha’awar fitowa takarar mukaman siyasa daban-daban a zaben 2019.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Shirye-shiryen jam’iyyar na Kasa, Austin Akobundu ya fitar, ta ya ce an fito da sayar da fam din a bisa ka’idoji da sharuddan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC ta gindaya.

Za a sayi fam na sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a kan naira miliyan 2, sai fam na neman fitowa takarar shugaban kasa shi kuma naira miliyan 10.

Gaba daya fam na takarar gwamna zai kama naira milyan 6, yayin da fam don takarar

Na Sanata zai kama naira miliyan 4, na Majalisar Tarayya kuma naira milyan 1.5. yayin da fam na takarar dan majalisar jiha kuwa naira 6,000.

Dukkan ‘yan takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da majalisar tarayya, za su sayi na su fam din ne a hedikwatar PDP da ke Wadata Plaza, a Abuja.

Su kuma ‘yan takarar majalisar jiha za su sayi nasu fam din a ofishin INEC da ke jihohin su.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an yafe wa dukkn ‘yan takarar mata biyan kudin fam na tsayawa takara.

PDP ta ce ta rage kudin takarar fam din majalisar tarayya, domin bai wa matasa damar shiga a dama da su cikin sha’anin mulkin kasar nan.

Share.

game da Author