Osinbajo ya umarci a sake fasalin aikin ‘yan sandan SARS

0

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya umarci Sufeto Janar na ’Yan sanda, Idris Ibrahim, da ya ruguza tsarin aikin ‘yan sandan SARS, ya sauya wa aikin fasali gaba daya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Talata, Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, ya bayyana cewa hakan ya taso ne sakamakon yawan korafe-korafen cin zarafin jama’a da ake yi cewa ‘yan sandan masu aikin hana fashi da makami na yi.

PREMIUM TIMES ta sha buga labaran cin zarafi da gallazawar da SARS ke wa jama’a tare da yawan tilasta wa mutane su ba su kudade.

Baya ga wannan, ‘yan Najeriya da dama sun sha shiga shafukan su na twitter, su na kiraye-kirayen a ruguza SARS, saboda a ganin su, barnar da suke aikatawa ta fi gyaran da su ke yi aibi.

Baya ga kiran a sake fasalin SARS, Osinbajo ya kuma yi kira ga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam da ta binciki duk wani mai korafi a kan SARS.

Daga nan kuma Osinbajo ya yi kakkausan gargadi ga Sufeto Janar da ya tabbatar ‘yan sandan SARS sun rika yin aiki a kan ka’idar da dokokin kasar na suka gindaya, tare da bada fifiko da yin taka-tsantsan da ka’idojin Kungiyar Kiyaye Hakkin Dan Adam na Kasa da Kasa.

Share.

game da Author