Oloyede ya soki batun neman rage kudin jarabawar JAMB

0

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa ya zuwa ranar 29 Ga Augusta, dalibai 24,148 ne suka samu nasarar shiga manyan makarantun kasar nan.

Daga nan kuma sai ya yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi, su na korafin a rage kudin jarabawa, a bisa dalilin su cewa sun yi yawa matuka.

Shugaban na JAMB ya ce masu yin wannan korfin ba su ma da wata hujja ko dalilin korafin, kuma ba za a ce kudin ma sun yi yawa ba.

Kimanin dalibai miliyan 1,662,762 suka rubuta jarabawar UTME ta neman shiga jami’a tsakanin watan maris, 9 zuwa 19 na cikin watan.

Kakakin Hukumar, Fabian Benjamin ne ya bada karin hasken yawan daliban da aka dauka zuwa manyan makarantu a cikin wata hira ta wayar tarho da ya yi da PREMIUM TIMES.

Har ila yau, Oloyede ya ce ai kudin jarabawar JAMB a Najeriya ya ma fi na kowace kasa a duniya arha.

Ya ce JAMB ta na saida fam din a kan naira 5,000, amma har naira bilyan 7.8 ta aika wa Gwamnatin Tarayya a matsayin kudaden shiga.

“Shin me ya sa ba za su nemi WAEC ko NECO su rage na su yawan kudin jarabawar ba? Me ya sa kuma bas u nemi NABTEB ta rage na ya kudaden jarabawar ta ba?

“Kawai don a yanzu an ga mu na ririta kudaden da muke samu ne, kuma su na isar hukumar gudanar da ayyukan ta, har ma a samu rarar kudade masu yawa. Shi ne a yanzu wasu ke cewa wai mu fito mu rage kudaden.” Inji Oloyede.

Share.

game da Author