Hukumar Kula da Masu Bautar Kasa (NYSC), ta bada hutun kwanaki uku domin fara zaman makokin daliban ta su tara wadanda ruwa ya ci a garin Mayo-Selbe, cikin Karamar Hukumar Gashaka a Jihar Taraba.
Daraktan Yada Labaran NYSC Adenike Adeyemi ce ta bayyana haka a cikin wata takardar da ta raba wa manema labarai a Abuja.
Adenike ta kara da cewa har a zuwa yanzu dai an iya gano gawawwaki bakwai, amma har yanzu ana neman sauran gawawwaki biyu.
Ta ce masu bautar kasar sun nitse cikin ruwan ne saboda malalar da ruwa ya kara yi a cikin kandamin da suke wanka a cikin kogin.
Ruwan inji Adeyemi, ya malala musu ne daga kan wani tsauni ba zato ba tsammani.
Ta ce wannan mutuwa ta gigita gaba dayan hukumar NYSC ta kasa, kuma ta na taya iyayen yaran jimamin rashin matasan masu yi wa kasa hidima da ka yi. “Don haka hukumar NYSC ta ware hutun kwanaki uku domin yin zaman makoki da jimamin rashin yaran su tara da aka yi.”
Ta ce hutun ya fara ne daga Litinin, 6 Ga Agusta.
A karshe ta ce za a sassauta tutar NYSC kasa-kasa a duk inda ta ke a kafe a fadin kasar nan.