A yau Talata ne rundunar ‘yan sandar jihar Ondo ta sanar cewa mutumin da ya yi mankasa da kwayar Tramadol ya rasu a babbar asibitin dake garin Owo ranar Litini.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo Femi Joseph ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sun kama wani mutumi dake sace mutane da ya yi mankasa da kwayar Tramadol a shagon siyar da magani a Akure.
Joseph ya bayyana cewa barawon tare da wani abokinsa sun je wannan shagon siyar da maganin domin sace mai shago amma sai ya yanke jiki ya fadi a kasa ya fara barci.
Ya ce tun da suka kama shi ranar 5 ga watan Agusta a mankas dinsa bai tashi daga barci ba.
” Bayan mun yi kokarin ya farka daga barci amma inaa, shine muka tattara shi muka garzaya da shi asibiti.
Jaridar ‘Punch Newspaper’ ta ruwaito cewa wannan mutum ya sha milligram 400 na kwayar Tramado ne shi ya sa yake ta sharba irin wannan barci.
Sai dai kuma wasu likitoci da muka zanta da su sun ce kwayar Tramadol ba ya sa mutum ya yi irin wannan barci mai tsawo haka. Sun ce kamata ya yi a gudanar da gwaji domin tabbatar da abin da ya sa wannan mutum da yake ta barci har na tsawon mako guda.
Akwai yiwuwa ya gauraya kwayoyin da yake sha da wasu kwayoyi amma bisa ga sanin mu Tramadol bata sa mutum barci irin haka.
Joseph yace kafin likitoci su iya farfado da wannan barayo yace ga garin ku nan bayan ya yi tsawon kawanki tara yana barci a gadon asibiti.
A karshe ya yi kira ga mutane musamman matasa da su guji shaye shayen miyagun kwayoyi.