Mataimakin kakakin majalisar dokokin Kaduna ya fice daga APC

0

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna dake wakiltar mazabar Kachia, John Audu ya fice daga jam’iyyar APC.

A wasikar da ya rubuta Audu ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin haka ne bisa ga rashin nuna adalci da ake yi a jam’iyyar.

Duk da cewa Audu bai fadi jam’iyyar da zai koma ba amma ya ce kafin ya yanke wannan hukunci sai da ya gana da mutanen mazabar sa game da haka.

” Daga ranar 7 ga watan Agusta na yanke shawara ficewa daga jam’iyyar APC. Wasu daga cikin dalilan da ya sa na hakura da jam’iyyar shine ganin yadda rashin adalci yayi mata katutu. Ni kuma ba zan iya ci gaba da zama a haka ba. Shine nayi shawara da mutanen mazaba ta na hakura kawai.

Haka shima dan majalisa dake wakiltar Kudan, Junaidu Yakubu, ya sanar da ficewa daga APC. Shima bai fadi ko wace jam’iyya zai koma ba.

Share.

game da Author