Mataimakin Gwamnan Akwa Ibom ba zai bi Akpabio APC

0

Mataimakin Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Moses Ekpo, ya karyata labaran da aka rika watsawa dangane da shi cewa ya sauka daga mukamin sa, zai fita daga PDP domin ya bi Godswill Akpabio zuwa cikin jam’iyyar APC.

Ya ce ba gaskiya ba ne sam da ake cewa ya sauka daga mukamin sa na mataimakin gwamna.

Haka nan Kakakin Majalisar Jihar Akwa Ibom Onofiok Luke da Sanata Bassey Albert da wasu mambobin majalisar jiha, duk sun karyata labarin fitar su daga PDP.

Gwamna Udom Emmanuel wanda ke gwamnan dan kabilar su Akpabio ne, shi ma bai bi sanatan zuwa APC ba.

Kakakin yada labarai na Mataimakin Gwamnan, Ekikere Umoh, ya ce kowa ya daina daukar batun da muhimmamnci, ya na mai cewa karya ce kawai.

Ya ce yanzu haka mataimakin ya na birnin New York, inda ya ke Wakiltar gwamnan jihar a taron al’adu na kasa da kasa da ake kira Ati Annang.

Ya ce bai ga dalilin da zai say a koma APC ba.

Share.

game da Author