KWALARA: Mutane 11 sun rasu a Kano

0

Cutar kwalara ya bullo a wasu kauyuka uku dake karamar hukumar Bebeji jihar Kano inda akalla mutane 11 suka rasu.

Mazauna wadannan kauyuka sun bayyana cewa a yanzu haka mutane 47 na kwance asibitin dake kusa da su.

Wani mazaunin karamar hukumar mai suna Ubale Dauda ya bayyana cewa mazauna kauyukan Kuki da Hayi ne suka fi kamuwa da cutar sannan hakan na da nasaba da rashin asibiti ne a kauyukan.

Sai dai kakakin ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Ismail Gwammaja ya bayyana cewa ma’aikatar su bata san da bullowar cutar ba a wadannan kauyuka sai dai gwamnati za ta matsa don ganin yadda za a tunkari abin da wuri.

Share.

game da Author