Kotun Daukaka Kara a Abuja, a yau Litinin ta jingine umarnin sammacen neman a kama Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
A ranar 8 Ga Agusta ne, Mai Shari’a Stephen Pam, na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bada umarnin a kama shugaban na INEC, saboda ya ki halartar zuwa kotun har karo uku.
Wannan tirka-tirka dai ta afku ne sakamakon wata shari’a da ta shafi siyasar jihar Anambra.
An kai wa kotun jihar Anambra kara ne cewa, wani dan siyasa mai suna Ejike Oguebego ya kalubalanci INEC a jihar Anambra, saboda ta ki bayyana shi a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar PDP, kamar yadda Kotun Kolin Najeriya ta bada umarni cikin watan Disamba, 2014.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa kotun daukaka karar dai a ranar Laraba ta jingine batun kamun da ta ce a yi wa Yakubu, kuma a dakatar da duk wata magana ko tankiya a kan shari’ar har sai an karkare da batun daukaka karar da INEC din ta yi.
Lauyan Yakubu mai suna Adeboyega Awomolo, ya tabbatar da rahotn cewa wannan umarni da Kotun Daukaka Kara ta bayar ya na nufin kotun da ake Babbar Kotun da ake shari’ar ba za ta ci gaba da sauraren karar ba, har sai bayan an karkare da batun daukaka karar da INEC ta yi.
“Ina tabbatar muku da cewa Kotun Daukaka Kara ta dakatar da umarnin kamun da ta ce a yi wa Shugaban INEC, har sai abin da ta zartas tukunna.”
Ya kara da cewa za a saurari karar da INEC ta shigar a ranar 17 Ga Agusta.