Wata Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja, ta yi watsi da karar aka shigar inda aka nemi kotun ta hana wato sanatoci yunkurin su na tsige Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa daga kujerar sa.
Tun bayan da Saraki ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma PDP ne wasu sanatoci suke ta matsa lambar ko dai ya sauka ko kuma tsige shi.
Cikin karar da Sanata Isa Misau da Rafiu Adebayo suka shigar, sun nemi kotun da ta tilasta wa mambobin majalisar dattawa su bi dokar kotu kada su kitsa duk wani shiri domin kokarin tsige Saraki, har sai bayan hukuncin da kotun ta yanke.
Tun farko dai Sanata Emeka Etiaba da Mahmoud Magaji ne suka shigar da kara ta hannun lauyan su cewa, su na son kotu ta fayyace wa duniya shin ko ficewar da Saraki ya yi daga APC ya cancanci a tsige shi ko a’a.
Shi kuwa Mai Shari’a Nnamdi Dimgba, ya karbi korafin mutanen biyu, sai dai kuma abin da ya zartas shi ne zai gaggauta sauraren korafin na su da kuma yin nazarin sa, maimakon ya umarci kada a kitsa duk wani shiri na tsige Saraki, kamar yadda suka nema kotun ta yi.