A yau Alhamis ne kotun dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa wani malamin makarantar Boko mai suna David Ikejiobi mai shekaru 29 hukuncin zama a kurkukun kirikiri saboda kama shi da laifin yi wa wata ‘yar shekara 13 fyade.
Dan sandan da ya shigar da karar Christopher John ya ce Ikejiobi ya aikata wannan ta’asa ne ranar 25 ga watan Maris a gidan ‘iyayen yarinyar dake Ijeshatedo jihar Legas.
John ya ce bayanai sun nuna cewa Ikejiobi na da masaniyar cewa iyayen wannan yarinya kan bar wa ‘yar su mukulin gidan su domin lokacin da take dawo makaranta iyayen basu taso daga wurin aiki ba.
” A nan sai wata rana Ikejiobi ya sato jiki ba biyo sawun wannan yarinya inda ya danne ta a cikin gidan.
John ya ce Ikejiobi ya sadu da wannan yarinya sau uku.
Bayan ya saurari haka alkalin kotun P.E Nwaka ya yi watsi da rokon sassauci da Ikejiobi ya yi Sannan ya yanke masa hukuncin zama a kurkukun kirikiri har sai an kammala shari’ar.
Za a ci gaba da shari’a ranar uku ga watan Satumba.
Discussion about this post