KIDAYA: USAID ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 11

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa USAID ta bada gudunmawar dala miliyan 11 domin tallafa wa aikin kidaya da hukumar NDHS za ta gudanar a wannan shekara.

Ya fadi haka ne a Abuja inda ya kara da cewa ma’aikatar kiwon lafiya tare da hadin gwiwar hukumar kidaya ta kasa (NPC) za su gudanar da haka.

Ya ce za a fara wannan kidaya ne ranar 15 ga watan Agusta zuwa 15 ga watan Disamba a duk jihohin kasar nan.

” Wannan itace karo ta shida da ake gudanar da irin wannan kidaya a Najeriya sannan duk sakamakon da za a samu za a yi amfani da shi wurin samar da ababen more rayuwa wa mutane har na tsawon shekaru biyar.

Adewole ya yi kira ga gidajen jaridu da su tallafa wa ma’aikatar kiwon lafiya da hukumar kidaya wajen wayar da kan mutane game da mahimmancin wannan kidaya.

A karshe jami’ar USAID Erin Holleran ta ce za su zauna su tattance sakamakon da za a samu daga kidayar domin sanin wasu fanoni ne ke bukatan a taimaka musu da wadanda ke bukatan a gyara su ne.

Share.

game da Author