Kananan ‘yan kasuwa miliyan biyu za su amfana da bashin kai-tsaye daga Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa za ta raba wa kananan ‘yan kasuwa lamunin karfafa sana’a da jari har su miliyan biyu.

Za a raba lamunin ne da karkashin tsarin tallafa wa masu karamar sana’a, da ake kira ‘Trader Moni’.

Raba kudaden da aka bayyana cewa daga yanzu zuwa cikin karshen shekarar nan za a fara shi, za a rai wa masu karamin jari lamunin naira 30, 000 ba tare da gindiya sharuddan gabatar da mai tsaya mas aba.

An dai kaddamar da wannan shiri a Lagos, cikin makon da ya gabata, inda za a rika raba wa marasa karfin jari naira dubu 30,000 a fadin jihohin kasar nan, har da Abuja.

Ana sa ran za a fara raba lamunin daga jihar Lagos, sai Kano, daga nan kuma sai jihar Abia.

bayanin ya kara da cewa a jihohi kamar Lagos da Kano masu yawan al’umma, ana sa ran wasun su daga jihohin za su ci moriyar sama da naira 30,000.

Tuni dai har an gama daukar sunayen masu rabon samun lamunin har 500,000.

An kuma tabbatar da cewa tuni Bankin Kasuwanci, wanda ta hannun sa ne za a raba lamunin, har ya dauki ejan-ejan 4000 da za su yi aikin tantance masu rabon karbar lamunin.

Shi dai wannan tsari na ‘Trader Moni’ an fito da shi ne domin a rika ba mai karamin karfi lamunin naira 10,000.

Zai daddage ya biya bashin a cikin watanni shida. Bayan ga biya kuma za a iya kara masa wani lamunin da ya kai naira 15,000 zuwa naira 50,000.

Share.

game da Author