Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa kafewa ko bushewar da Tafkin Chadi yay i, kara rura wutar ayyukan ta’addancin Boko Haram a Yankin Arewa maso Gabas.
Amina ta ce Tafkin Chadi ya kasance gagarimin wurin neman abinci da sana’o’i na miliyoyin jama’a.
Amina ta yi wannan karin haske ne a birnin Stockholm yayin da ta ke bude taron Makon Ruwa na Duniya da ake gudanarwa a kasar Sweden.
Daga nan sai ta bada labarin kalubalen da ta fuskanta da kuma darasin da ta dauka a lokacin da ta ke Ministar Harkokin Muhalli, kuma shugabar Majalisar Samar da Ruwa da Tsaftace Muhalli.
“Na tashi a yankin Arewa maso Gabas a Najeriya, inda rashin tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli suka zama manyan kalubalen yankin gaba daya.
“Tafkin Chadi na daya daga cikin manyan hanyoyin da mutanen yankin kusan milyan 30 suka dogara domin samun abinci da inganta tattalin arzikin su na karkara.
“A yau kuwa kusan kashi 90 bisa 100 na ruwan Tafkin Chadi ya kafe. Wasu ma na ta yin kintacen cewa nan da karshen wannan karnin tafkin shafewa zai yi gaba daya, a neme shi a rasa.
“Wannan kafewa da Takin Chadi ya yi da kuma matsalar kwararowar hamada a Arewa, ta hargitsa komai a yankin, kama daga kasuwanci, noman rani da kamun kifi. “Sannan kuma abin ya haifar da matsalar tsaro, kiwon lafiya da karancin abinci. To duk wadannan matsalolin sun tattaru sun haifar da rashin tsaro a yankin ta hanyar barkewar rikici da masu mummunar ra’ayin-rikau.
Amina ta kuma nuna takaicin yadda kananan yara ‘yan kasa da shekara biyar akalla 340,000 ke mutuwa a kowace shekara ta hanyar gudawa, saboda rashin muhalli mai tsafta, rashin tsaftar ita kan ta da kuma rashin ruwan sha mai tsafta.
Wannan inji ta, ya nuna kusan yara 1000 ke mutuwa kenan.
Ta ci gaba da cewa kimanin kashi 40 bisa 100 na mutanen duniya su na fama da matsalar karancin ruwa, yayin da wasu milyan 844 na fama da matsalar ruwan sha sannan kuma sama da biliyan biyu ke shan ruwa marar tsafta a bisa tilas, don ba su da wani zabi.
A karshe ta yi nuni da cewa a fadin duniya, idan ana fama da karancin ruwan amfani ko na sha ko na noma, to mata ne da kananan yara suka fi shan wahala.
Discussion about this post