Wani matashi mai shekaru 28, Muhammed Isa ya bayyana cewa zai yi tattaki tun daga garin Legas zuwa Abuja domin nuna bacin ran sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APc mai mulki.
Shi dai Mohammed Isa dan asalin jihar Barno ne mazaunin garin Legas.
Ya fara wannan tattaki ne daga gadar Otedola sannan ya na rike a hannun da wata yar karamar akwatin gawa cewa da zarar ya isa garin Abuja zai nemi wani asibiti da ke ajijar gawa a jiye masa wannan akwati cewa, gawar APC a ciki, ta mutu ta zama gawa.
Da yake hira da manema labarai kafin ya kama hanya ya bayyana cewa ya na cike da bakin ciki ne da fushin shugaba Buhari da jam’iyyar sa cewa har yanzu bai ga abu daya da suka yi alkawari sun cika ba tun da aka kafa wannan gwamnati.
” Tun da jam’iyyar APC ta hau mulkin kasar nan farashin man fetur ya tashi, sannan aikin da suka ce za su samar mana mu matasa miliyan uku, ya gagara, kai 500,000 ma da aka ce za a iya samar wa matasa abin ya gagara.
” Sannan kuma ni Isah Mohammed ba zan zabi PDP ba domin duk kanwar ja ce. Wani matashi zan yi wa kamfen a 2019.
Idan ba a manta ba a shekaran 2015 Isa ya yi tattaki daga Legas zuwa Lokoja domin taya gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello murnan zama gwamnan jihar da Buhari, kuma yace ko a wancan lokaci babban dalilin da ya sa yayi haka shine ganin cewa Buhari zai iya dawo da martabar Najeriya, ashe duk rudu ne.
” Ina yin da na sani zaben APC da Buhari da nayi domin shekaru uku sun wuce babu canjin da muka sa ran samu koda ko daya ce lafiyayya cikin alkawurran da aka yi mana sai dai bakar wahala da tsadar rayuwa da muke fama da su. Saboda haka gani nan na kamo hanya daga Legas zuwa Abuja da akwatin gawa ta dauke da gangar jijin APC.”