Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kara yi wa sabbin jam’iyyu 23 rajista, a yanzu daf da gabatowar zaben 2019.
Gidan Talbijin na Channels ya kuma ruwaito cewa INEC ta kara wa’adin dakatar da yin rajistar katin shaidar yin zabe zuwa sati biyu, bayan ranar 17 Ga Agusta da ta gindaya rufewa tun da farko.
INEC ta gayyaci Shugabannin Jam’iyyun tare da Sakatarorin su da su hallara a hedikwatar hukumar a ranar 16 Ga Agusta, domin su karbi kwalin shaidar yi musu rajista.
Ya zuwa yanzu dai akwai jam’iyyun siyasa har 91 kenan wadanda ke da muradin tsayawa takarar shugabancin kasa, da kuma neman mukamai daban-daban a zaben 2019.