Idan Kwankwaso ya isa ya zo Kano ya kaddamar da takarar shugaban kasar sa – Ganduje

0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa kanawa sun dade da wancakalar da tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya ce idan har Kwankwaso ya isa ya shigo garin Kano ya kaddamar da kamfen din sa na neman shugabancin Najeriya da yake shirin yi.

” Muna da damar mu wancakalar da shi, kuma mun riga mun yi watsi da shi tuni.

” Ba mu taba daukar sa dan takarar shugaban kasa ba kuma ba za mu taba yin haka ba. Dan takarar shugaban kasan mu daya ne tak kuma shine Shugaba Muhammadu Buhari.

” Mu mutanen Kano zamu yi amfani da duk wata dama da muke da ita domin nuna masa iyakar sa, sannan mu tasa keyar sa mu nuna masa hanyar waje rod tun kafin zabe ma ta zo.

Ganduje ya amayo wadannan kalamai ne a wajen kaddamar da shirin baiwa mata 6,600 tallafin jari na 15,000 domin bunkasa sana’o’in su.

An yi rabon wannan tallafi ne a gidan gwamnati dake Kano ranar Lahadi.

Share.

game da Author