HARAJIN ILMIN FIRAMARE DA SAKANDARE: Idan Amarya ba ta hau doki ba!

0

Ranar Alhamis da ta gabata aka gudanar da Taron Majalisar Kolin Harkokin Ilmi ta Kasa, karo na 63, a Abuja. A wurin taron dai an fito da wani shiri da Gwamnatin Tarayya ta fara tunanin dora wa iyayen daliban sakandire da firamare harajin kudin makaranta na tilas.

Idan da an amince da wannan tsari, iyayen yara za su rika biyan kudin makaranta a kan tsarin yawan ‘ya’yan ka, yawan harajin da za ka rika biya na kudin makaranta.

Gwamnati ta shigo da wannan tunani ne inda aka tattauna batun a Taron Majalisar Majalisar Kolin Harkokin Ilmi ta Kasa, karo na 63. Da farko har an rigaya an rattaba amincewa da shigon da tsarin biyan harajin, amma da gardama ta tirnike, tilas aka cire batun aka jingine shi gefe.

Idan da an amince da wannan tsari, to za a rika biya wa ‘yan firamare naira 500 kowane yaro, yayin da su kuma daliban sakandare za a rika biya wa yaro naira 1000.

Bayanin da ke kunshe da batun harajin wanda da farko aka rattaba amincewa da shi, ya nuna cewa za a rika biyan kudaden a cikin wani asusu da tuni har sun yi gaggawar rada masa suna ‘‘Asusun Tara Harajin Dalibai”.

Sai dai kuma ana tsakiyar taron sai wani babban jami’in harkokin ilmi wanda da ya mike bai ambaci sunan sa ba, ya ce idan har aka fito da tsarin biyan harajin ‘yan makarantar firamare da sakandare, to fa an karya dokar da ta kafa tsarin bayar da ilmi kyauta na bai daya, wato Dokar UBEC ta 2004.

Shi kuma Karamin Ministan Ilmi, Anthony Anwukah, cewa ya yi batun kudin harajin dalibai abu ne da ya ke bukatar ya bi matakai ana tattauna shi, domin Hukumar na tattauna hanyoyin samar da harkokin ilmi kudade.

“Duk da cewa Dokar UBEC ta 2004 ta ce a bayar da ilmi kyauta, amma ai wannan doka za a iya yi mata ‘yar kwaskwarima ta yadda za a iya magance matsalar kudaden gudanar da harkokin ilmi a kasar nan.” Wannan jawabi na ministan na nuna cewa gwamnati na goyon bayan fito da tsarin biyan harajin daliban kenan.

Shi ma Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilmi, Sunny Echono, cewa ya yi dalibai da iyaye ne ya kamata su daki nauyin taimakawa harkokin ilmi a kasar nan. Sai dai kuma saboda an kasa cimma matsaya daya, tilas aka cire wannan batu, aka jingine shi.

INA ALKAWARIN BAYAR DA ILMI KYAUTA?

Wannan yunkuri na neman yanka wa iyayen yara harajin karatun ‘ya’yan su a makarantun firamare da sakandare da aka tattauna a ranar Alhamis, ya bai wa dandazon ’yan jaridar da ke wurin mamaki, domin kowa ya tabbatar da irin alkawarin da gwamnatin APC ta yi a lokacin kamfen cewa da zaran ta hau mulki, to ilmin kyauta ne, tun daga firamare har zujwa jami’a.

Baya ga wannan alkwarin, akwai alkawarin ciyar da ‘yan firamare, wanda ya zuwa wannan mako da ake ciki gwamnatin tarayya ta ce an ciyar da dalibai milyan 8.5. Wannan shiri ya na fuskantar kalubale, ga shi kuma har yau a wasu wuraren ba a ma san ana yi ba.

Akwai kuma wani babban alkawari da APC ta yi cewa ta na hawan mulki ba tare da bata lokaci ba, za ta bi ilahirin makarantun sakandire na yankin jihohin Arewa-maso-Gabas ta zagaye su da Katanga, sannan kuma ta bi gaba dayan su a makala musu kyamara mai gani har hanji, domin magance matsalar tsaro.

Wannan alkawari kuwa ya na neman zama tatsuniya, domin har yau ba a kara tada labarin sa ba, wasu kuma sun ma manta da cewa an yi shi.

A zaman yanzu tun daga biro da fensari da kayan litattafan karatu, duk iyayen yaro ke saye. Inda Allah ke kawo sauki musamman mu a nan Arewa, shi ne da ake samun wasu masu hannu da shuni ko kungiyoyin tsoffin dalibai da ke taimaka wa wasu makarantu da kayan aiki.

Gwamnonin jihohi a karkashin Mulkin Muhammadu Buhari sun samu kudi fiye da gwamnonin baya. Don me ba su kara wa ilmin firamare da na sakandare kasafin kudade kamar yadda Hukumar UNESCO ta shar’anta a rika kashe wa bangaren ilmi a kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya ba.

Yawanci ayyukan da wasu gwamnoni ke yi, duk ayyukan Baban-giwa ne, wadanda Bature ke kira ‘white elephant project’, da ba su tasiri kai tsaye ga inganta rayuwar al’umma.

Kusan kashi 99.5 na manyan ma’aikata da masu rike da mukamai na siyasa, babu wanda dan sa ko ‘ya’yan sa ke karatu a sakandare ko firamare ta gwamnati. Daga wadanda ‘ya’yan su ke karatu a kasashen waje, sai wadanda ke biya wa yaron sa daya kudin makarantar wata uku kacal ya kai albashin sa nan a shekara daya, har ma da alawus din sa na shekara gaba daya.

Mai yiwuwa wadanda suka bijoro da wannan batu na biyan harajin ‘yan makaranta, sun manta da cewa an yi wancan alkawari na bayar da ilmi kyauta a karkashin gwamnatin APC.

Daga shekarun nan uku na mulkin APC, har yau dai jihohin Arewa su ne a sahun baya wajen karatun ilmin sakandire mai inganci.

Irin haka fa aka yi wa talakawa romon-kunne da romon-baka, aka sa suka jefa kuri’a da niyyar za a zaftare kudin litar man fetur. Amma bayan an hau ba da dadewa ba, sai aka kusa ninka farashin litar, daha naira 86 zuwa naira 147.

Ya kamata gwamnati ta sani cewa, bijiro da wannan batu na yanka wa talakawa harajin karatun ‘ya’yan su a wannan lokaci bai dace ba. Domin idan jam’iyyar adawa ta tsinci wannan babban makami, to za ta yaki gwamnati da shi sosai. Kun san kuwa talakawa mara mata baya za su yi.

Kai, ko ba komai dai ya kamata gwamnatin APC ta fahimci cewa idan amarya ba ta hau doki ba, to ba fa zai yiwu a dora mata kaya ba!

Share.

game da Author