HADARIN MOTA: Mutane uku sun kone kurmus a jihar Kogi

0

Wani Jami’in hukumar kiyaye haddura ta (FRSC) na jihar Kogi Bisi Kazeem ya bayyana cewa a dalilin wata mummunar hadarin mota da aka yi a hanyar Abuja- Lokoja mutane uku sun kone kurmus.

Kazeem ya bayyana haka wa manema labarai a Lokoja inda ya kara da cewa hadarin ya auku ne da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Ya ce motoci uku masu kirar Toyota Carina, Scania Truck da Tankar Mack suka yi karo da juna.

” Duk motoci ukun sun kama da wuta sannan mutane uku sun kone kurmus, biyar kuma sun sami rauni, daya ya tsira bai ji ciwo ba.

Kazeem yace mutane biyar din da suka sami rauni na samun kula a asibitin ‘Federal Medical Center’ dake Lokoja.

Bayanai sun nuna cewa babbar titin Okene zuwa Lokoja daga Abuja na daya cikin manyan tituna a kasar nan da ake yawan samun hadarukka kasar nan.

Share.

game da Author