Gwamnatin Tarayya ta fara tunanin dora wa iyayen daliban sakandire da firamare haraji

0

Gwamnatin Tarayya ta fara tunanin dora wa iyayen daliban sakandire da firamare harajin kudin makaranta na tilas.

Idan da an amince da wannan tsari, iyayen yara za su rika biyan kudin makaranta a kan tsarin yawan ‘ya’yan ka, yawan harajin da za ka rika biya na kudin makaranta.

Gwamnati ta shigo da wannan tunani ne a yau Alhamis, inda aka tattauna batun a Taron Majalisar Majalisar Kolin Harkokin Ilmi ta Kasa, karo na 63.

Da farko har an rigaya an rattaba amincewa da shigo da tsarin biyan harajin, amma da gardama ta tirnike, tilas aka cire batun aka jingine shi gefe.

Idan da an amince da wannan tsari, to za a rika biya wa ‘yan firamare nira 500 kowane yaro, yayin da su kuma daliban sakandare za a rika biya wa yaro naira 1000.

Bayanin da ke kunshe da batun harajin wanda da farko aka rattaba amincewa da shi, ya nuna cewa za a rika biyan kudaden a cikin wani asusu da tuni har sun yi gaggawar rada masa suna ‘‘Asusun Tara Harajin Dalibai”.

Sai dai kuma ana tsakiyar taron sai wani babban jami’in harkokin ilmi wanda da ya mike bai ambaci sunan sa ba, ya ce idan har aka fito da tsarin biyan harajin ‘yan makarantar firamare da sakandare, to fa an karya dokar da ta kafa tsarin bayar da ilmi kyauta na bai daya, wato Dokar UBEC ta 2004.

Shi kuma Karamin Ministan Ilmi, Anthony Anwukah, cewa ya yi batun kudin harajin dalibai abu ne da ya ke bukatar ya bi matakai ana tattauna shi, domin Hukumar na tattauna hanyoyin samar da harkokin ilmi kudade.

“Duk da cewa Dokar UBEC ta 2004 ta ce a bayar da ilmi kyauta, amma ai wannan doka za a iya yi mata ‘yar kwaskwarima ta yadda za a iya magance matsalar kudaden gudanar da harkokin ilmi a kasar nan.” Wannan jawabi na ministan na nuna cewa gwamnati na goyon bayan fito da tsarin biyan harajin daliban kenan.

Shi ma Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilmi, Sunny Echono, cewa ya yi dalibai da iyaye ne ya kamata su daki nauyin taimakawa harkokin ilmi a kasar nan.

Sai dai kuma saboda an kasa cimma matsaya daya, tilas aka cire wannan batu, aka jingine shi.

Share.

game da Author