Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta umarci korarren shugaban DSS, Lawan Daura ya tura jami’an hukumar su mamaye Majalisar Tarayya har su hana ‘yan majalisar shiga ba.
Daga nan kuma sai ya bayyana mamayewar da aka yi a matsayin karya dokar kasa da duk wata dokar duniya mai tasiri da tafarki na dimokradiyya.
Ya ce wannan haramtacciyar mamaya an yi ta ne ba da masaniyar fadar shugaban kasa ba. Don haka babu yadda za a yi fadar ta amince da wannan karya doka da rana kata.
Kakakin Yada Labaran Osinbajo, Laola Akande ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya fitar ga manema labarai.
Daga nan sai ya yi alkawarin cewa duk wani wanda ke da hannu a wannan hawan-kawara da aka yi wa Majalisar Tarayya, sai an zakulo shi, kuma za a hukunta shi, ko wane ne.
Babu ruwan ‘yan sanda – Sufeto Janar Idris
Shi ma Sufeto Janar na ‘Yan sanda Ibrahim Idris, ya nesanta rundunar ‘yan sandan Najeriya daga mamayewar da aka yi wa Majalisar Dattawa.
Idris ya ce ba shi da masaniyar za a kai mamayar, ba a umarce shi ba kuma ba a tura ‘yan sanda su mamaye majalisar ba.
Idris ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya gana da Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa, yayin da aka yi musu kiran gaggawa, shi da Lawan Daura.
Sufeto Janar din ya ce abin ya je masa ya na cike da mamakin yadda za a tura jami’an tsaro su mamaye Majalisa ba tare da sanin sa ba.
Daga nan sai ya yi tir da wannan mamaya da aka yi wa majalisa, har ya kara da cewa zai fitar da bayanin matsayar Hukumar Tsaro ta ‘yan sanda dangane da abin da ya kira take ;yancin dimokradiyya da aka yi tare kuma da karya doka.
‘Mu ma babu ruwan mu’- APC
Ita ma jam’iyyar APC ta nesanta kan ta daga mamayar da jami’an tsaro na DSS suka yi wa Majalisar Dattawa a safiyar yau Talata.
Jam’iyyar wadda ita ce ke mulki, ta ce ba da masaniyar ta ko amincewar ta aka kai mamayar ba.
A baya dai an rika yayata wani shirin tuggu da aka danganta da cewa sanatocin APC 30 sun gana da korarren shugaban DSS Lawal Daura a Abuja ranar Litinin da dare, inda aka shirya tuggun yadda za a tsige Saraki.
Discussion about this post