Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nemi Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Wike, ya ce Magu a ko ta wane dalili ya cancanci tsigewa, bisa karambanin sa na toshe asusun jihohin Benuwai da Akwa-Ibom da ya yi.
“Ina kira da a gaggauta cire Shugaban Riko na EFCC, Ibrahim Magu, saboda yunkurin sa na hambare gwamnatin jihohi har biyu da ya yi.
“Don kawai Magu ya yi saure ya bude asusun ajiyar saboda an matsa masa lamba, wannan bai hana cewa ya aikata laifi.”
Haka Wike ya shaida wa ‘yan jarida wannan kalami ne gidan gwamnatin jihar Rivers, Fatakwal.
“Idan ka toshe wa Gwamnatin Jiha Asusu, ai ka yi wa gwamnatin jihar juyin mulki kenan domin wannan zai tsaida ayyukan gwamnatin jihar na majalisa, kwamishinoni da alkalai. To me kuma ya rage wa Magu idan ya yi haka?
Wike dai ya kara da cewa idan har za a tsige Darakta Janar na SSS saboda ya kai hari a Majalisar Tarayya, to shi ma Magu na EFCC ya cancanci tsigewa a bisa kasassabar toshe asusun jihohi har biyu da ya yi.
Ya ce saboda EFCC ejan ce ta gwamnatin APC, shi ya sa ba ta tashi rufe asusun Benuwai ba sai da Gwamnan Jihar ya fice daga APC masu EFCC a hannu, ya koma PDP.
Sannan kuma Wike ya danganta rufe asusun Akwa-Ibom da ficewar da Godswill Akpabio ya yi daga PDP ya koma APC.
Ya yi kira ga kungiyar gwamnonin Arewa da su tashi tsaye su kare dimokradiyya daga hannun ‘yan bunburutu.