Gobara ya babbake fitaccen kasuwar kifi dake Baga, jihar Barno

0

Gobara ya babbake fitaccen kasuwar kifi dake Baga, jihar Barno inda shaguna da kifi da aka ajiye don siyarwa suka kone kurmus a kasuwar.

Wani mai dan kasuwar ne mai suna Muhammad Labo ya bayyana haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litini.

Labo yace akwai yiwuwar wayoyin wutan lantarki ne ya yi sanadiyyar aukuwar gobarar.

” Bayan an tashi da kasuwa kowa ya tafi gida sai kwatsam muka ji wannan mummunar labari. An rasa dukiya na miliyoyin naira.

A karshe kakakin hukumar kashe gobara na jihar Barno Ambursa Pindar ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa sun yi amfani da tankunan ruwa hudu sannan suka iya samun nasarar taro wutar.

Share.

game da Author