Dalilin da ya sa Buhari ba zai yi saurin daukar mataki kan Minista Kemi ba – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa har yanzu kima da darajar Shugaba Muhammadu Buhari wajen kyamatar rashawa da zamba na nan daram, duk kuwa da zargin da ake yi wa Ministar sa ta Harkokin Kudade, Kemi Adeosun da mallakar satifiket na NYSC na bogi.

Mohammed ya yi wannan bayani ne yayin da kai ziyara ofishin jaridar Authority a jiya Litinin da yamma.

Ya ce dalilin da ya sa Buhari ba zai yi gaggawar kora ko dakatar da minista Kemi ba, saboda hukumar da abin ya shafa na kan bincike, don haka ba zai yi azarbabin shiga cikin sha’anin wata hukuma ba, musamman ganin ana bincike.

Lai ya ce idan Shugaba Buhari ya yi gaggawar daukar wani mataki a yanzu, tamkar riga-Malam-masallaci ne aka yi.

“Ku tuna fa zargi ne fa aka ce ake yi mata, kuma hukumar da abin ya shafa ta na bincike. Shi ma Shugaba Buhari ya san ana bincken.

“Sannan tunda an ce zargi ne, sai a jira sakamakon bincike kenan. Kuma shi zargi ai dama ba wannan ne karo na farko da aka fara yin zargi a tarihi ba. Shi kan sa Buhari an yi masa a baya, da aka ce wai ba ya da satifiket na kallama sakandare.

“Ni ma fa an sha zargi na da maganganu na bogi iri daban-daban. Ko kwanan nan ma an ce wai direba na ya ci burki, mu na cikin tafiya kan titi, ya ce wai ya canja jam’iyya, ya bar ni a kan titi cikin mota zaune.’’

Daga nan sai Lai ya ci gaba da bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samar musamman ga masu karamin karfi a kasar nan.

Ya ce zuwa yanzu ana biyan marasa galihu su 400,000 alawus na naira 5,000 kowane wata.

Sannan kuma an dauki matasan da suka kammala digiri 200,000 aikin N-Power, kuma za a kara daukar wasu adadlin haka kwanan nan.

Akwai kuma ramcen kudaden jari da aka ba mata masu kasuwanci, masu sana’o’in hannu da sauran sana’o’i na naira 50,000 wasu kuma har naira 100,000.

Share.

game da Author