Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya harzuka, kuma ya nuna fushin sa dangane da yadda wasu sojojin Najeriya ke juya baya a guje su ne tsere wa maharan Boko Haram.
Buratai ya ce duk sojan da aka kama ya kara tserewa daga bata-kashin yaki da Boko Haram, zai dandana kudar sa.
Babban Hafsan dai ya raba wa kwamandojin sojojin kasa wasu ka’idojin kafsa gumurzu, kuma ya hada da gargadin cewa duk wani kwamandan da ya juya baya ya dade keya daga musayar wuta da Boko Haram, to ya kuka da kan sa.
Daftarin ka’idojin kafsa gumurzun dai sun kai shafuka har 180, ya aika su ne ga dukkan kwamandoji na kowane mataki, bataliya da sansanonin sojojin kasar nan a duk inda suke a wuraren da ake fafata yakin tsawon shekaru tara da Boko Haram a fadin Arewa-maso-Gabas.
Wannan gargadi dai wani kakkausan raddi ne ga sojojin, bayan fuskantar mummunan kisa da sojojin suka dandana a hannun Boko Haram kwanan nan.
Akalla an yi asarar rayukan manyan sojoji biyu da sauran na kasa da shi har su 43 tsakani 13 zuwa 26 Ga Yuli. Wannan kuwa ana ganin babban koma baya ne da ya jefa manyan hafsoshin sojojin kasar nan cikin matukar damuwa.
ZAFAFAN KALAMAN BURATAI
“Abubuwan da suka faru kwanan nan a cikin zaratan ‘Operation Lafiya Dole’, inda wasu sojoji suka nuna tsoro suka arce a lokacin gumurzu da Boko Haram, ba tare da sun tsaya kare-jini-biri-jini ba, to abin damuwa ne, domin hakan ya nuna sojojin da suka tsere din a amatsayin wadanda ba su kware sosai ba kuma matsorata.”
“Wannan abin haushi da suka tafka zai iya sallace duk wani karsashi na gagarimar nasarar da aka samu a kan yaki da Boko Haram.
“To daga yau duk wani kwamandan da ya gudu a lokacin da abokan gaba suke musu barin wuta, har gudun na sa ya janyo asarar rayuka da makamai, to za a yi masa hukunci mai tsananin gaske, kamar yadda aka gindaya a cikin Dokokin Aikin Soja.
“Kowa ya sani kuma zan kara tunatar da ku cewa dokar ta ce duk sojan da ya nuna razana ko tsoro a wurin yaki, to hukuncin sa kisa ne, ko kuma wani hukunci mai tsananin gaske. Wannan ya danganta ma ga irin laifin da ya aikata.”
Majiyar sojoji da dama ta tabbatar wa PREMIUM TIMES sahihanin wannan wasika mai dauke da kakkausan gargadi ga sojoji, kwanaki kadan bayan dan taratsin kare hakkin jama’a, Deji Adeyanju ya fallasa wasikar a shafin san a twitter.
MARTANIN WASU KWAMANDOJI
Yayin da Kakakin Sojojin kasar nan ya ki cewa komai a kan wannan wasika, su kuma kwamandojin da aka aika wa wadannan wasiku, su na kallon wasikar kamar “tsoratarwa ce, karkatar da su ne daga abin da suke yi, kuma abin damuwa ne a wurin su.”
Sojojin da aka zanta da su, kuma suka nemi a boye sunayen su domin kada a hukunta su, saboda ba su da iznin yin magana da ‘yan jarida.
Sun nuna cewa Buratai gaba daya ya kauce daga ainihin abin da ya kamata a duba kan dalilin kisan sojojin da aka yi a ’yan kwanakin nan a hannun Boko Haram.
“Shi ne ya kamata ya rika kawo rahotanni na leken asirin halin da Boko Haram ke ciki ga mayakan sojoji. Amma sau da yawa sai ya rika cewa an murkushe Boko Haram gaba daya.”
Wani kwamanda cewa ya yi akwai karancin kayan fada a hannun su a halin yanzu.
“Dukkan motocinn yakin mu da tankoki samfurin T72, wadanda aka sayo a lokacin mulkin Jonathan, wannan gwamnatin ta kasa rike su hannu biyu. Mafi yawa sun lalace, ba su ma iya gyaruwa ko da an gwada gyarawar.
“Ana kawo mana daukin karin dakarun yaki sau da yawa a makare, idan ma sun zo din kenan.”
Ya ce dalili kena wasu lokutan sukan nemi turo musu karin sojoji daga kasashe makwauta.
“Ku dubi dai yadda sojojin Kamaru su kan garzayo kawo mana dauki tun daga tsawon kilomita 60 tsakanin mu da su. To sun fi mu kayan yaki, shi ya sa mu ke rokon su kawo mana agajin gaggawa.”
A cikin watan Yuli dai Boko Haram sun kashe sojoji 45, kuma sun fatattaki sojoji, suka kutsa cikin sansanin su, suka kwashi makamai da abinci mai tarin yawa. Akalla kuma an ji wa wasu sojoji 50 mummunan rauni.
Har iya yau kuma ana ci gaba da kashe fararen hula, yayin da ake neman wasu sojojin a rasa bayan Boko Haram sun yi musu kwanton bauna.
A yanzu Boko Haram cikin watan Yuli, sai suka fi bayar da karfi wajen kai hare-hare kai tsaye a sansanonin sojoji, wanda rabon da irin haka ta faru, tun cikin Oktoba, 2016, lokacin da suka kashe sojoji a sansanin Kogin Komadogou, a jihar Yobe.
Duk da cewa wasu kwamandoji da sojojin da aka kai wa hari, sun shaida wa PREMIUM TIMES akwai matsalar rashin wadataccen kayan abinci, makamai da kuma yanke musu kudaden alawus din su da ake yi, a daya bangare, hukumomin sojoji sun kaddamar da binike kan wannan korafe-korafen, amma har yau ba a bayyana sakamakon bincike ba.
Makonni kadan bayan wasu hasalallun sojoji sun nemi yi wa kwamandan Sansanin Maimalari dukan tsiya a cikin Disamba, 2016, bayan ya bar su a tsakiyar fagen yaki, kwanaki biyu bai tura musu abinci ba.
Sai kuma cikin Nuwamba, 2017, wasu sojoji da ke bakin daga suka yi wa PREMIUM TIMES korafin cewa an shiga makonni da dama ba tare da an biya su kudaden alawus din su ba. Dama kuma kudaden, a ta bakin su, ba su wadace su ba.
GAGGAWAR SANARWAR KAKKABE BOKO HARAM
Wata majiya kuwa ta bayyana akwai matsala dangane da yadda Buratai ke gaggawar sanar da samun nasarar kakkabe Boko Haram, wannan kuwa ya na bai wa mayakan Najeriya wata fuska biyu kenan – a daya bangare ana ewa an kakkabe Boko Haram, a wani bangare kuma su dai sun sai akwai sauran rina a kaba.
“Don haka ba ma fa matsalar rashin wadataccen abinci ko isassun makaman yaki da Boko Haram ba ne, ko batun karancin kudaden alawus. Kowa ya sakankance an bayyana cewa an murkushe Boko Haram.” Haka wani kwamandan soja ya bayyana.
Dokar soja Sashe na 47 dai ta tanadi hukunci ga duk sojan da ya juya a lokacin gumurzu ya arce. Sai dai kuma duk da haka, a cikin wannan sashen akwai inda aka yi karin bayani cewa akwai inda idan abu ya kai ya kawo, za ka sanin yadda ka yi, ka tsira da ran ka, ko don saboda sake gwabza fada da kai a gaba.