Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi hutun kwanaki 10 a Landan. Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwa cewa Buhari zai tafi hutun ne jibi Juma’a, kuma ya mika mulki a hannun mataimakin sa Yemi Osinbajo.
Cikin sanarwar da aka fitar a shafin twitter na Fadar, an bayyana cewa Buhari zai fara hutun ne daga gobe Alhamis, kuma tuni ya mika mulkin ga Osinbajo, domin tafiyar da zai yi a ranar Juma’a, 3 Ga Agusta, 2018.
“Kuma an rigaya an aikata da wasikun sanarwa cewa ga Shugaban Majalisar Dattawa da na wakilai, Bukola Saraki da Yakubu dogara, inda aka sanar da su fara hutun, tafiya Landan yin kwanaki 10 da kuma mika mulki ga Yemi Osinbajo.
“Hakan kuwa bin umarnin da dokar kasa ta gindaya ne, a Sashi na 145 (1) na dokar 1999.
Discussion about this post