Bindow ya cike gurbin kwamishinonin sa biyu da suka koma PDP

0

A yau Litinin ne gwamnan jihar Adamawa Mohammed Bindow ya cike gurbin kwamishinoni biyu da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP kuma suka ajiye aikin su.

Wadanda suka ajiye aiki sune, kwamishinan filaye Yayaji Mijinyawa da kwamishinan Harkokin kasuwanci Umar Daware a dalilin ajiye aiki da suka yi da kansu suka kuma canza sheka zuwa PDP.

A jawabin bankwana da yayi wa wadannan kwamishinoni biyu ya yaba da irin gudunmuwar da suka ba gwamnatin jihar sannan yayi fatan alheri.

Gwamna Bindow ya cike gurbin wadannan kwamishinoni ne da Usman Tukur daga karamar hukumar Fufore da Iliyasu Bello daga karamar hukumar Yola ta Arewa.

Share.

game da Author