BARNO 2019: Allah zai zabi mai gado na, ba ‘yan siyasar Abuja ba -Gwamna Shettima

0

Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima, ya bayyna cewa ba shi masaniyar wanda zai canje shi, a matsayin gwamnan jihar bayan wa’adin sa ya kare a watan Mayu na 2019 mai zuwa.

Kashim ya ce ya bar wa Allah ya zabar wa al’ummar jihar wanda ya fi dacewa.

Sai dai kuma ya jaddada cewa wanda zai gaje shi din zai kasance ba mai yawan shekaru ba ne, zai kasance daga cikin ‘yan siyasa masu tasowa.

Ya ce wannan lamarin kuwa bai yi wa wasu ‘yan-siyasar-Abuja ‘yan asalin jihar dadi ba.

‘Ni Kashim Shettima, b azan iya zabar wa al’ummar jihar Barno gwamna da zai yi mulki baya na ba. Allah ne kadai zai iya yin haka.”

“Ko mutum ya na so, ko ba ya so, Allah ya rigaya ya kaddara wanda zai zama gwamna a jihar Barno.

Shettima ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da karbi bakuncin kwamishinonin sa da suka je gidan gwamnati domin amsa gayyatar gwamnan ta cin abincin rana.

Sai dai kuwa wadannan kalamai sun nuna cewa ana wani irin zama da za a ce ta-ciki-na-ciki ne kawai a tsakanin mambobin APC na jihar Barno.

Wannan bikin Sallah shi ne na karshe da Gwamna Shettima ya yi a kan mulki.

Wannan magana ta a ta kasance wani raddi ne ga wasu gungun manyan ‘yan siyasar jihar mazauna Abuja, da suka nuna rashin son ganin wani daga cikin sabbin-yanka-raken siyasa ya zama gwamnan jihar. Su a ganin su, daga cikin tsoffin-‘yan-alewa ya kamata a fitar da gwamnan jihar Barno.

“Su ‘yan siyasar Abuja da ke cewa a yau Barno ta fada a hannun kananan yara, bari a tuna musu cewa ai a lokacin da wasun su suka yi gwamna, ko shekaru na ma bas u kai ba.” Inji shi.

Amma har aka yi taron aka tashi, Shettima bai yi magana a kan muradin san a zama sanata mai wakiltar Barno ta tsakiya ba, mukamin da Baba Garbai ne a kai, kuma makusancin siyasa ne na gaske ga gwamnan.

Shi ma Garbai din ya halarci zaman walimar.

A halin da ake ciki a siyasar APC a jihar Barno, tun daga na can kasa har kwamishinoni da kowa, ba wanda zai ce ga wanda zai iya kasancewa shi ne dan takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyya mai mulki.

Shi ya sa da yawan wadanda suka halarci walimar tare da gwamna, sun je ne a bisa tunanin a wannan ranar za su samu karin haske daga bakin gwamna.

Sai dai kawai abin da za su iya tantancewa daga kalaman gwamnan shi ne, sabon gwamnan jihar Barno zai kasance daga cikin sabbin-‘yan-yanka-raken siyasar Barno, ba daga cikin tsoffin-‘yan-alewar siyasar jihar ba.

Gwamna Shettima ya rika yi musu jawabai tamkar wasiyya, ya na mai ce musu wannan ce walimar Sallah ta karshe da ya shirya musu a matsayin san a gwamna.

Ya bayyana kalubalen da ke gaban su da kuma gaban jihar baki daya. Daga nan kuma ya yi cikakken jawabin nasarorin da aka samu a jihar a karkashin jam’iyyar APC.

Share.

game da Author