Babu wanda ya yi wa Shehu Sani alkawarin Kujerar sanata a PDP – Jam’iyyar PDP

0

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna Hassan Hyet ya bayyana cewa ya yi mamaki matuka game da furcin da sanata Shehu Sani da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya ke yi cewa wai jam’iyyar PDP ta yi masa alkawarin tikitin kujeran sa idan har zai dawo jam’iyyar.

Ya fadi haka ne ranar Talata a Kaduna inda ya bayyana cewa mutane da dama sun yi ta kiran sa domin samun karin bayani kan haka da ke ta yayadawa.

” Ina mai tabbatar muku babu wanda ya yi wa sanata Shehu Sani alkawarin tikiti. Sannan idan ma an yi haka ofishina ne kawai zata iya haka kuma ba ayi ba, sannan ba kuma za a yi ba.

Ya ce kada wani ya yarda da wannan rudi da hayagaga na mutane.

Yace jam’iyyar PDP za ta yi maraba da Shehu Sani idan ya amince ya dawo jam’iyya amma ya sani cewa idan ya dawo zai nemi kuri’un mutane kamar yadda kowa zai yi wajen samun kowace kujera da yake so ya dare.

Share.

game da Author