Gwamnatin Tarayya ta tsaida ranakun Talata da Laraba, 21 da 22 Ga Agusta a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah ta 2018.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka, ranar Alhamis, a Abuja, a cikin jawabin da Babban Sakataren Ma’aikatar ya sa wa hannu a madadin sa.
Yayin da ya ke wa daukacin ‘yan Najeriya muryar zuwan Babbar Sallah, Dambazau ya kuma yi kira da a yi amfani da wannan lokaci da rungumi juna cikin kauna da kuma nuna sadaukarwa wajen hada kai a kasa tare da kawo ci gaba.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya a gida da waje da su goya wa gwamnatin Muhammdu Buhari baya, a kan kudirin da ta sa gaba na kara dangon zaman lafiya da hada kan al’umma a Najeriya.