An zabi Nuhu Shadalafiya sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna

0

A yau Laraba ne majalisar dokokin jihar Kaduna ta zabi Nuhu Shadalafiya sabon mataimakin kakakin majalisar.

Nuhu na wakiltar Karamar hukumar Kagoro a majalisar dokokin.

Majalisar da gudanar da wannan zabe ne bayan kakakin majalisar Aminu Shagali ya sanar cewa mataimakin kakakin majalisar na da John Audu ya sauka daga kujeran sa.

Ya ce Audu ya gabatar da wasikar haka ne ranar Talata.

Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne mataimakin kakakin majalisar wanda ke wakiltan Kachia John Audu ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Audu y ace ya yanke hukuncin haka ne bisa dalilin rashin nuna adalci da ake yi a jam’iyyar.

” Daga ranar 7 ga watan Agusta na yanke shawara ficewa daga jam’iyyar APC. Wasu daga cikin dalilan da ya sa na hakura da jam’iyyar shine ganin yadda rashin adalci yayi mata katutu. Ni kuma ba zan iya ci gaba da zama a haka ba. Shine nayi shawara da mutanen mazaba ta na hakura kawai.”

Share.

game da Author