An saki Lawal Daura, amma an kwace masa fasfo

0

Jami’an leken asiri sun saki korarren Babban Daraktan DSS, Lawal Daura, bayan an kwace masa fasfo. Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.

An sako shi jiya Laraba da yamma, daga gidan da ya ke a tsare, wanda jami’an SSS ne ke kula da shi, a Gwarimpa. A can ya ke tsare tun lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bada odar a sallame shi daga aiki.

An bada umarnin a tsare shi bayan wasu zarge-zargen da aka ce ya aikata wasu laifuka da suka shafi cin amanar kasa da kuma kawo barazana ga tsaron kasa.

Da farko an bayar da rahoton cewa ya na tsare ne a Guzape, can a ofishin SARS a Abuja, inda ya dade ya na amsa wasu muhimman tambayoyi a hannun ‘yan sanda.

Daga nan kuma an rika yawo da shi, daga wannan gida zuwa wancan a cikin Abuja. Daga nan an adana shi a wani gida da ke Gwarimpa, haka wata majiyar jami’ann tsaro ta shaida wa PREMIUM TIMES.

“An damka masa wayar tarho din sa, kuma aka ce ya tafi abin sa. Amma an kwace masa fasfo, yadda ba zai iya fita kasashen waje ba.”

“Ba a san takamaimen inda ya ke ba, amma dai babu yadda za a yi ya iya sulalewa ya gudu, tunda akwai sa-ido sosai a kan sa.”

Ana kuma sa ran zai fuskanci caji daga tuhumar da ake yi masa.

Share.

game da Author