An kashe ‘yan sanda 30 cikin wata daya – Kwamishina

0

An kashe akalla ‘yan sanda 30 da suka sadaukar da rayukan su a wurin yi wa kasar su aiki a cikin wata daya a Najeriya.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Akwa- Ibom, Adeyemi Ogunjemilusi ne ya bayyana haka a ranar Talata a garin Eket, yayin da ya ke magana wurin taron masana kan tsaro.

Karamar Hukumar Eket ce ta shirya taron tare da hadin-guiwar Rundunan ‘Yan Sandan Jihar.

“Mun rasa jami’ai 30 a kasar nan a cikin wata daya kacal.”

Ya ci gaba da cewa ‘jami’an ‘yan sanda na sadaukar da rayuwar su a kowace rana, amma abin takaici, an fi maida hankali wajen ganin laifin wasu kalilan daga baragurbin ‘yan sanda, wadanda ke bata wa hukumar suna.

Daga nan sai ya ce an kama mutane har 60 da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne kwanan nan a lokacin da aka yi wani fada tsakanin kungiyoyin asiri biyu.

“Laifi ne babba wani ya zo ya ce ka shiga kungiyar asiri kafin ya ba ka aiki.”

Daga nan sai ya ce duk wanda aka kama da laifi kotu za ta hukunta shi.

Sai dai kuma ya ce akwai matasa da dama wadanda a shirye suke da su watsar da mummunar dabi’ar da suka jefa kan su ta shiga kungiyar asiri, kuma su na so su shiryu, su zama nagari.

Share.

game da Author