Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wata mai suna Hadijat Kabir da laifin kitsa sace ta don ta damfari mijin ta naira miliyan 15.
Bisa ga bayanan da kwamishinan ‘yan sandan jihar Edgar Imohimi ya ba da, ya ce Hadijat ta shirya haka ne da wasu mutane.
Mijin Hadijat mai suna Kabiru ne ya kawo karar sace matar sa. Ya ce an sace ta ne a hanyar ta na zuwa asibiti tare da ‘yar su.
” Kabiru ya bayyana mana cewa wasu mutane sun kira shi ta waya suka ce sun yi garkuwa da matarsa suna bukatar ya kawo miliyan 15 kafin su sake ta.
” Jin haka ke da wuya sai mu kuma muka fantsama farautar wadannan mutane.”
Imohimi ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa sace Hadijat din da aka yi na karya ne domin sun gano cewa Hadijat da wadannan mutane na zaman su ne a kauyen Ado-Odo dake karamar hukumar Ota jihar Ogun.
” Bayan mun kama su sai Hadijat ta bayyana cewa itace ta shirya a sace ta sannan ta yi haka ne domin ta sami kudi daga wurin mijinta Kabir.
” Hadijat ta ce mijinta Kabir marowaci ne da ya mallaki gidaje da kudi a Legas sannan duk da cewa ta haifan masa ‘ya’ya hudu baya kula da ita yadda ya kamata.
Bayan haka daya daga cikin masu garkuwan da ‘yan sandan suka kama tare da Hadijat mai suna Ahmed Kudus ya ce bashi da hannu a aikata wannan aiki da Hadijat ta shirya.
Ahmed yace ya fara haduwa da Hadijat kwanki biyar da suka wuce a lokacin da ta zo neman ‘ya’yan sa Lukuman.
” Na taya wana ne wajen kiran mijin Hadijat a waya amma bayan haka ba ruwa na.