An kama manyan dillalen miyagun kwayoyi hudu a jihar Gombe

0

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Gombe Shina Olukolu ya bayyana cewa dakarun sa sun kama wasu dillalen miyagun kwayoyi hudu a jihar.

Olukolu ya fadi haka ne ranar Alhamis a garin Gombe inda ya kara da cewa rundunar ta kama wadannan mutanen da miyagun kwayoyi da dama a tare da su.

Ya ce bayanan da suka samu game da su wadannan mutane ne ya sa suka sami nasarar kama su.

” Cikin kwayoyin da muka kama su da shi sun hada da kwayoyin Tramadol, Vallium, Dizapam, Exzol, Kodin da madaran su kodai’’.

A karshe Olukolu ya ce za su gurfanar da su a kotu da zaran an kammal bincike a kan su.

Share.

game da Author