An bindige wani jigon APC a gidan kallon kwallo

0

Jiya da dare ne aka bindige wani jigo a cikin jam’iyyar APC, a gidan kallon kwallo, yayin da ake kallon wasa tsakanin Manchester United da kuma Leicester.

An harbe Bunmi Ojo ne a unguwar Ajitadidun da ke cikin Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Kafin rasuwar sa, Ojo ya yi aiki a matsayin sakatare da tsohon gwamnan jihar, Segun Oni.

Wadanda aka yi kisan a gaban su, sun tabbatar da cewa makasan sun harbe shi a kai, sannan suka gudu, yayin da gidan kallo kuma kowa ya yi kan sa a guje.

Ojo ya taba rike mukamin kwamishina a Hukumar Da’ar Ma’aikata ta Kasa.

Jam’iyyar APC a jihar ta bayyana kisan a matsayin kisan gilla, kuma ta yi ta’aziyyar mamacin.

Jam’iyyar ta ce ba za ta samu damar hutu ba har sai an gano makasan Ojo tukunna.

Shi ma gwamna mai jiran gado, Fayemi, ya bayyana kisan da cewa dabbanci ne, kuma ya shafe hasken murnar cin zaben da jam’iyyar ta yi a ranar 14 Ga Yuli.

Share.

game da Author