Abin da ya sa muke neman naira biliyan 189.2 don zaben 2019 -INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana sahihan dalilan hukumar na neman naira biliyan 189.2 domin zaben 2019.

Ya bayyana haka a yau Laraba yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin zaben 2019 a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC a Abuja.

Na farko dai ya fara da samun karin yawan jam’iyyun siyasa da aka yi, karin yawan masu jefa kuri’a, karin farashin ayyukan kai-da-komo, tashin-gwauron-zabin dalar Amurka da sauran kudaden Yuro fa Fam na Ingila da kuma uwa-uba karin yawan mazabu da kuma rumfunan zabe.

A zaben 2015, INEC ta kashe naira biliyan 120, amma a wannan zabe na 2019, ta na neman naira biliyan 189.2.

A takaice kenan an samu kari na naira bilyan 69 kenan idan aka kwatanta zaben 2019 da na 2015.

Da ya ke fayyace dalilan dalla-dalla, Yakubu ya ce, jam’iyyu 44 suka shiga zaben 2015, amma a yanzu akwai jam’iyyu har 91 da za su shiga zaben 2019.

Ya ce karin yawan jam’iyyu zai kara fadi da tsawo takardun kuri’un da ake dangwalawa, sannan a kara yawan layuka a cikin shafukan takardun.

“Sannan idan aka lura za a ga aiki jawur zai karu wajen sa-ido da yin duba-garin yadda jam’iyyun siyasa har 91 za su rika gudanar da zabukan fidda-gwanin su da kuma tarukan gangamin su.

“Mu na da mazabu 12,558, kenan sai INEC ta bi diddigin har na sau 141,778.”

Baya ga wannan, Yakubu ya bayar da dalilai na karin kudin man fetur idan aka kwatanta da zaben 2015.

“Sannan kuma a yanzu muna da yawan mazabu fiye da zaben 2015. A yanzu an kara samun mazabu har 68, sannan kuma ga karin rajistar masu zabe.

“Sai mun kara daukar ma’aikata wucin-gadi, ya zuwa ranar 11 Ga Agusta mun yi wa mutane milyan 12.1 rajista.

Mambobin kwamitin sun yi nazarin ko su amince da abin da INEC ta nema, wato a ba ta kudin bai daya a yanzu, ko kuma a yi abin da Shugaba Muhammadu ya nema, wato a fara bai wa INEC naira biliyan 143.5 a yanzu, sauran naira biliyan 45.6 kuma, a jinkirta sai 2019.

Sai dai ita kuma INEC ta nemi a ba ta kudin gaba daya a yanzu.

Share.

game da Author